Wednesday, 14 February 2018

"Ni bance maciji yaci kudi ba: karya aka min">>Inji wadda ake tuhuma

Matarnan ma'aikaciyar hukumar shirya jarabawar shiga jami'a, Jamb a takaice, ta karyata maganar da aketa yayatawa cewa wai tace maciji ya hadiye kudi miliyan talatin da shida, Philomena, kamar yanda ake kiranta, ta bayyanawa kafar watsa labarai ta CNN cewa sharri aka mata domin ita ba haka tace ba.


Ta kara da cewa itafa karamar ma'aikaciyace wadda aikinta kawai shine sayar da katin amma hakkin bayar da ba'asin kudi ba a kanta yake ba, tace tana aikine a karkashin daraktoci wadanda sune ya kamata ace sun fara bincikarta kamin wani na waje ya bincike amma sai kawai mikata hannun jami'ai akayi ba tare da an binciketa a cikin ma'aikatar tasu ba.

Wannan labari dai na cinye kudi da maciji yayi ya matukar dauki hankulan mutane sosai a ciki da wajen Najeriya.

No comments:

Post a Comment