Tuesday, 20 February 2018

'Nifa bance Buhari be tabuka komaiba: Hanyar zuwa garinmu ta lalace, ban gayaraba, 'yar Aduwa yazo be gayara, Jonathan yazo be gayara, amma Buhari ya gyara'>>Obasanjo

Da alama dai tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya dawo yana goyon bayan gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin kuwa a jiyane mukaji wani yabo da Obasanjon yawa Gwamnatin Buhari akan bayar da lasisin gina matatun mai masu zaman kansu.


Wannan yabon da yayiwa shugaba Buhari yasa wasu suka fara kiranshi da sunaye ganin cewa a watan daya gabata ya cewa Buharin ya hakura da neman takara, amma Obasanjon ya fito ya wanke kan shi, inda yace shifa ba wai yace dama gwamnatin Buhari bata tabuka komai ba, misali, titin Legas zuwa Ibadan da kuma titin dake zuwa garin su Obasanjo din, Ogun duk sun lalace, tun lokacinshi be gayara ba, 'Yar Aduwa yazo be gyara ba, Jonathan yazo be gayara ba amma gashi Buhari ya gyarashi.

Saboda haka yace Gwamnatin shugaba Buhari tayi abubuwan yabo.

No comments:

Post a Comment