Thursday, 8 February 2018

Nima nayi shiru>>General BMB

Da alama an kashe Boss gaba daya, kowa ya bada kai a fadan cacar baki da habaice-habaice daya barce cikin kwanaki biyu da suka gabata tsakanin manyan taurarin fina-finan Hausa, a jiyane dai mukaji labarin sasanta tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango, to dama dai ance manya gyaran wasa, da alama yanzu kowa yabi, har Bello Muhammad Bello da abin yafi yin zafi ta bangarenshi ya fito yace shiru dai yafi akan mayar da martani dangane da wani abu da aka yiwa mutum.


Muna musu fatan Alheri da kuma Allah ya kara musu fahimtar juna baki daya.

No comments:

Post a Comment