Friday, 9 February 2018

Nura M. Inuwa ya samu k'aruwar diya mace

Masu iya magana na cewa, idan kaji an fara ambaton abu to ga dukkan alamu abun ya kusa tabbata ko kuma yana kan hanya, a jiyane, tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa ya fito ya karyata labarin cewa matarshi ta haihu, cikin ikon Allah sai gashi yau kuma ta haihun da gaske inda aka samu diya mace.Nura ya bayyana a dandalinshi na sada zumunta cewa ya samu karuwar diya mace a tayashi da addu'a.
Muna fatan Allah ya albarkaci rayuwarta da sauran yara baki daya, ita kuma mahaifiyarta Allah ya kara mata lafiya.

No comments:

Post a Comment