Thursday, 1 February 2018

Rarara ya zambaci Kwankwaso a cikin sabuwar wakar shi, saboda soke zuwa Kano da yayi

Tauraron mawakin siyasa, Dauda Kahutu, Rarara ya fitar da wata sabuwar waka inda ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zambo a ciki, dalilin fasa zuwa Kanon da yayi.


Kamar dai yanda shafin Rariya suka tuwaito, taken sabuwar wakar ta Rarara shine "Mahadi ya firgita ya ki zuwa kano", ranar talatar data gabatane, 30 ga watan Janairu, akayi tsammanin zuwam Kwankwason Kano amma saboda irin sarkakkiyar dake cikin ziyarar tashi da kuma alamun cewa idan yaje za'ayi tashin hankali 'yan sanda suka bashi shawarar soke ziyarar tashi.

Da farko dai Kwankwason ya dage sai yaje, amma kwana daya kamin ranar ziyarar sai ga sanarwa cewa ya soke ziyarar tashi saboda shawarwari daga magabata.

A cikin wakokin da Rarara yayi na neman takarar shugabancin kasar shugaba Buhari dai yabon Kwankwaso ya rikayi amma yanzu da alama ya canja sheka.

Ga kadan daga cikin abinda Rarara ke fadi a cikin wakar tashi.

"Allah Ya Maimaita Mana Mulkin Ganduje, Mu Mun San Kai ba Mugu Bane, Tsula Kullum Shi Sai Mugun Nufi Ga Shi da Tsoro Ga San Tsokana", Cewar Dauda Kahutu Rarara.

No comments:

Post a Comment