Friday, 16 February 2018

Rashida Mai sa'a ta bayar da tallafin kayan abinci ga mabukata

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Amarya, me baiwa gwamnan Kano shawara a kan harkokin mata, Rashida Adam Mai'sa'a ta kaiwa mutanen wani kauye kayan tallafin abinci karkashin gidauniyarta ta tallafawa gajiyayyu.A wasu hotuna da ta wallafa a dandalinta na sada zumunta da muhawara, anga Rashida da sauran mukarrabanta suna rabon kayan abinci ga matan kauyen da suka ziyarta. Muna fatan Allah ya karba ya kuma saka mata da alheri.No comments:

Post a Comment