Sunday, 4 February 2018

Sarkakkiya ta shigo a wasikar IBB zuwa ga shugaba Buhari: Wata sabuwar sanarwa ta fito da IBBn ya nesanta kanshi da sanarwar farko

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida(IBB) ya fitar da wata sabuwar sanarwa inda ya nesanta kanshi da sanarwar farko da me magana da yawunshi, Kassim Afegbua ya fitar da farko da take cewa IBB din yace shugaba Buhari kada ya tsaya takara a zaben 2019 kuma kada 'yan Najeriya su zabeshi.A cikin sabuwar sanarwar IBB din yace waccan magana ra'ayin  marubucin takardarne, watau me magana da yaun nashi amma bashi ya fadi haka ba, IBBn ya kara da cewa idan yana so ya aika wani sako zuwa fadar shugaban kasa, a matsayinshi na tsohon shugaban  kasa yana da hanyoyin da zaibi sakonshi yaje kai tsaye ba tare da ya hada da 'yan jarida ba.

Sannan kuma ya bayyana cewa irin abubuwan dake guna a Najeriya suna barazana ga kasancewar kasar kasa daya al'umma daya, lura da irin siyasar da ake tabkawa da kuma rikice-rikicen dake faruwa tsakanin kabilu.

Saidai me magana da yaun IBB din a wata hira da gidan talabijin na Channels yayi dashi ya hakikance cewa waccan sanarwa ta farko daya fitar ba a radin kanshi ya fitar da itaba, saida tsohon shugaban kasar ya saka mata hannu kuma ya bashi umarnin fitar da ita.

Ya kara da cewa koda bayan da aka fitar da sanarwar ta biyu dake karyata ta farkon saida ya sake tuntubar me gidan nashi kuma ya tabbatar mai da cewa waccan sanarwar ta farko itace ta ainihi.

Ya kara da cewa bayan fitar da sanar war farko wasu abokan tsohon shugaban kasar suna ganin kamar yana so sukar ko kuma adawa da shugaban kasa me cine amma  abin ba haka yake ba, shiyasa suka je sukayi kokarin fito da sanarwar ta biyu.

No comments:

Post a Comment