Monday, 26 February 2018

Satar 'Yan makarantar Dapchi: Abin kunya baya karewa a Najeriya

Karanta ra'ayin wani bawan Allah akan satar 'yan matan makarantar garin Dapchi da 'yan Boko Haram sukayi mutumin yayi tambayar ta yaya aka sace mutane har dari kuma aka fita dasu zuwa kasar waje amma gwamnati bata sani ba, anya tana da karfin da ake zato kuwa?.


Abun kunya baya karewa 'Yan Nigeria

Saboda sanin yakamata da rashin sanin madosa, ace wai har a dauki mutum sama da hamsin 50+ a fitar dasu cikin Nigeria amma kuna matsayin Gwamnatin mai cikakken karfi, Gwamnati Shakumdun, ku keda idanuwa tako ina acikin fadin kasata Nigeria. Idanuwanku suna kallon ko'ina da Ina acikin kasata Nigeria. Amma har kuyi sakaci a sace 'yan mata 100+ baku sani ba, sannan afita da wasu zuwa wata kasa, Tawace hanya aka bi dasu aka ketare kasata Ngeria dasu, Kuna ina aka fita dasu, ina hukumomin dasuke kula da bangaren iyakar kasa, menene amfaninsu.

 Haba, kunada karfin damuke zato kuwa? kodai labari kawai mukeji irin labaran Yara!!!

No comments:

Post a Comment