Thursday, 1 February 2018

SHEKARU HUDU DA RASUWAR SHEIK ALBANY ZARIA

Ranar 1-2-2014 tafiya ta kamani daga Gombe zuwa garin Jalingo a jihar Taraba, ban dawo Gombe ba sai wajen misalin karfe 12 na dare,  kasancewar ni idan zanyi tafiya ina kashe wayoyina saboda tsaro, ashe a wannan daren mahaifiyata tana ta kirana a waya don ta sanar dani labarin shahadar Malami masoyina Sheikh Albaniy Zaria da ya faru a daren, wayana kuma bai shiga, sai bayan na bude wayar mahaifiyata ta kira ni cikin kuka take sanar da ni shahadar Malam Albaniy Zaria.


A wannan daren da aka hallaka Malam Albaniy Zaria banyi tsammanin za'a samu wani musulmi a Nigeria wanda yaji labarin kuma ya iya bacci a wannan daren ranar ba.

Allahu Akbar Yau shekaru hudu kenan cif Allah (T)  Ya azurta Malam Albaniy Zaria da shahada insha Allah tare da matarsa da 'dansa.

Bayan makiyanmu sunyi sanadin rabamu da malami masoyi insha Allah baccin da aka hanamu kadai a wannan dare mai dunbin tarihi da hawayen da aka sa muka zubar ba zai tafi a banza ba.

Wato su bayin Allah na kwarai idan sun kusan barin duniya Allah Yakan saka musu wannan ilhama a ransu, jama'a ku nemi karatuttukan Malam Albaniy Zaria da ya gabatar karshe karshen rayuwarshi zaku gaskata cewa Malam Albaniy Zaria waliyin Allah ne, yayi jawabai masu ma'ana ya bayyana sirruka masu fa'ida ga Nigeria kamar dai yana mana bankwana da duniya ne

Lokacin da 'yan ta'addan da suka tare motar Malam Albaniy Zaria akan hanyarshi na komawa gida daga wajen karantarwa, Malam Albaniy bai tsaya haka ba fita yayi daga cikin motar domin ya kare iyalanshi babu tsoro babu makami koda reza balle allura ya tunkaresu, anan suka dinga zazzaga mishi bullet, Malam Yabar duniya yana maimaita kalmar shahada

Salon kisan da akayiwa Malam Albaniy Zaria abune da aka dauki lokaci ana tsara yadda za'a aiwatar da kisan, domin zamu iya fahimtar cewa har kiran waya akayi a tsakanin wadanda suke yiwa makisan leken asiri cewa gashinan ya kammala karatu yana kan hanyar komawa gida ya biyo ta hanya kaza kuje ku tareshi ta gurin.

Hm! Wallahi ina tabbatar mana idan binciken kisan Malam Albaniy za'ayi ina da yakinin abune mai sauki a iya gano wadanda suka dauki nauyin kisan, wanda ya jagoranci kisan kamar yadda ya fadi da bakinshi shima tuni yabar duniya bayan an guntule mishi kafa daya sakamakon harbin da jaruman sojojin Nigeria suka masa a garin Mubi, bai gama jinya ba maigidansa yaci amanarsa ya tura aka hallakashi saboda tsoron juyin mulki.

Jama'a kunsan dabi'ah irin tamu na 'dan adam duk lokacin da nakai ga tunanin abin bakin ciki da zalunci da akeyi a wannan Kasa tamu Nigeria sai kuma na tuna cewa dadin abindai dukkan wani abu mai rai a duniya zai mutu, kuma sai Allah Ya sake tayar damu ya mana hisabi a gurin da babu wajen buya.

Ya Allah muna rokonKa Ka jikan Malam Albaniy Zaria tare da matarshi Ummu AbdulBarri da 'danshi, Allah Ka yafe musu laifukansu Allah Ka karbesu a matsayin shahidai.
Rariya.

No comments:

Post a Comment