Monday, 19 February 2018

Shugaba Buhari ya gana da wata kungiya a Daura: Yace duk kadarorin da aka kwace daga hannun mahandama sayar dasu za'ayi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da wata kungiya daga fadar sarkin Daura da suka kaimai ziyara a gida shi dake can Dauran, a jawabin da yayi musu yace kadarorin da aka kwato daga hannun wasu batagarin ma'aikata na gwamnati za'a sayar da sune a saka kudin a baitul mani dan amfanar 'yan kasa baki daya.Yace bazai sake yin kuskuren da yayi lokacin yana mulkin soja ba, wanda duk kadarorin daya kwato a wancan lokacin, bayan hambarar da gwamnatinahi aka mayarwa da wasu miyagun ma'aikatan da cin hanci da rashawa yawa katutu.

Da yake magana akan abubuwan da gwamnatinshi ta kawo na cigaba, Shugaba Buhari yace an samu tsaro musamman a yankin Arewa maso gabas sannan kuma yaji dadi da ganin yanda matasa da dama suka rungumi harkar Noma da gwamnatinshi ta kawo.

Yayi alkawarin cigaba da samar da kayan noma dan kara habaka harkar.

No comments:

Post a Comment