Sunday, 18 February 2018

Shugaba Buhari ya gaza: Inyamurai ya kamata a baiwa shugabancin Najeriya a 2019>>Inji Balarabe Musa

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa shugabancin kasarnan ya kamata a baiwa 'yan kabilar Inyamuraine a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu, yayi wannan jawabine lokacin da jaridar The Sun tayi wata ganawa dashi.


Balarabe Musa yace Hausawa da Yarbawa sune matsalar Najeriya domin su suka jawowa Najeriya ci bayan da ta ke fama dashi a yanzu, yace kabilar Inyamurai sunfi kowace kabila son kasancewar Najeriya zama kasa daya, yakin basasa da akayi ne da ya daidaita yankinsu yasa suke son ballewa.

Dan gane da samar da dan takara da dattijan Arewa sukeyi kuwa yace abin bazaiyi Nasara, domin dan kare muradun kansune suko son fiddo da dan takarar bawai dan ci gaban mutane ba, domin samun wanda zai maye shugaba Buhari ya kuma yi aikin da yafi na shugaba Buhari ba karamin jan aiki bane.

Yace bawai yana goyon bayan shugaba Buharin bane, Asalima idan zai fadi gaskiya shugaba Buhari bai yi abinda ake tsammanin zai yiwa 'yan Najeriya, ya gaza, amma a hakan, samun madadinshi sai an tona.

No comments:

Post a Comment