Saturday, 24 February 2018

Shugaba Buhari ya mayarwa da kungiyar da tace cin hanci ya karu a karkashin mulkinshi martani: Yace besan da wane irin bayanai sukayi aiki ba

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mayarwa da kungiyar nan ta Transparency International me saka ido akan yanda gwamnatocin kasashen Duniya ke gudanar da mulki, kungiyar dai tace cin hanci ya karu a Najeriya a karkashin mulkin shugaba Buhari amma yace bai san da wane irin bayanai sukayi amfani ba wajan cimma wannan matsaya tasu ba.


Shugaba Buhari a wata sanarwa da me magana da yawunshi, Garba Shehu ya fitar ya ce ya kasa gane da irin alkaluma da kuma bayanan da kungiyar tayi amfani dasu wajan cewa cin hanci da rashawa ya karu a Najeriya ba.

Shugaba Buhari yace a lokacinshine aka binciki mutanen da a da ake tunanin shafaffu da maine, irin su manyan jami'an tsaro da Alkalai da sauransu kuma hakan yasa mutane ma'aikata da dama sun shiga taitayinsu musamman masu hali irin na rashawa da cin hanci, shugaba Buhari yace ya kawo tsarin Asusun bai daya na gwamnatin tarayya wanda shima ya matukar rage yawan cin hanci a kasarnan.

Haka kuma a karkashin gwamnatinshine dai hukumar yaki da yiwa arIkin kasa zagon kasa ta EFCC ta kwato kudi masu dan karen yawa, haka kuma saboda irin namijin kokarin da shugaba Buharin yake yi wajan yaki da cin hanci da rashawa kungiyar kasashen Afrika ta bashi jagoran yaki da cin hanci a nahiyar, amma duk kungiyar bata ga wadannan abuba.

Shugaba Buhari ya kara da cewa kuma gwamnatinshi ta saka hannu da kasashen Duniya wajan yaki da cin hanci da rashawa, ya kara da cewa koda yake ita dai gaskiya sunan ta gaskiya koda wani zaice be gantaba ko kuma bazai yi amfani da ita ba.

No comments:

Post a Comment