Tuesday, 20 February 2018

Shugaba Buhari ya mika sakon gaisuwa ga iyalan Sheikh Abubakar Tureta

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika sakon gaisuwa ga iyalan marigayi, Sheikh Abubakar Abdullahi Tureta, a sakon da me magana da yawun shugabannkasar, Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya bayyana Marigayin malamin a matsayin me halayya ta gari da kuma son zaman lafiya.


Shugaba Buhari yace, Rasuwar Sheikh Abubakar ba karamin rashi bane akayi ta fannin Ilimi, yayi kira ga almajiran malamin da suyi koyi da kyawawan halayensa.

A karshe yace yana mika ta'aziyyarshi ga iyalan mamacin.

Muna fatan Allah ya jikan malam, idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da Imani.

No comments:

Post a Comment