Wednesday, 14 February 2018

Shugaba Buhari Ya Mika Ta'aziyyarsa Ga Gwamnatin Bauchi Kan Rasuwar Daliban Jihar

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyarsa ga Gwamnatin jihar Bauchi da kuma iyayen yara 21 Daliban Makarantar Sakandare dake Misau da suka rasa rayukansu da kuma malamansu.


Sudai wadannan Daliban da Malamansu uku (3) sun rasu ne a jiya Talata 13/2/2018 a wani hadarin mota da ya faru akan hanyarsu ta komawa gida daga Kano bayan da suka kai ziyarar karin ilmi da ake kira a turance da Excursion. 

Motar da take dauke da Daliban da malaman su ta yi taho mu gama ne da wata motar a Karamar hukumar Gaya dake Jihar ta Kano wanda hakan ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane 11 maza da kuma mata 10 wadanda dukkaninsu Daliban makarantar jeka ka dawo ce dake garin Misau ne.

Haka kuma mutuwar ta rutsa har da malamansu uku dake cikin motar.

Shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya gafarta musu ya kuma baiwa iyalansu, gwamnatin jihar Bauchi da al'ummar jihar baki daya hakurin jure rashin. Amin.
rariya.

No comments:

Post a Comment