Tuesday, 27 February 2018

Shugaba Buhari yace jam'iyyarshi ta APC ta shiryawa zaben 2019 da kyau

A daren jiyane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jagoranci taron jigogin jam'iyyar APC da ya faru wanda ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Farfesa, Yemi Osinbajo da shugaban jam'iyyar John Oyegun da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara da Bola Ahmad Tinubu dadai sauran manyan jam'iyya.A jawabin da yayi a gurin taron shugaba Buhari yayi kira ga manyan jam'iyyar da cewa su kula wajan gudanar da zaben fitar da 'yan takara ayishi yanda ya kamata dan kar a fada irin abinda jam'iyyar Adawa take ciki.

Ya kara da cewa ganin hukumar zabe ta fitar da lokutan da za'ayi zaben shekarar 2019 ya kamata jam'iyyarsu ta shirya kuma ayi zabe me inganci domin dama ita APC ansanta da yin zaben gaskiya.

Wannan bayani nashi yasa mutane suka rika mishi fassarar cewa da alama zai sake tsayawa takarar shugaban kasa.

No comments:

Post a Comment