Friday, 23 February 2018

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da harin Dapchi yayi alkawarin hukunta wadanda suka aikata shi ya kuma taya iyayen 'yan matan da aka sace jaje

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta hannun me magana da yawunshi, Garba Shehu yayi Allah wadai da harin da aka kai garin Dapchi  na jihar Yobe inda maharan suka yi gaba da yara 'yan mata 'yan makaranta, shugaba Buharin yacce yana jin wannan mummunan labari ya shirya wani kwamiti na musamman dan suje su gani da ido abinda ya wakana a wannan gari.


Haka kuma yace ya baiwa hukumomin tsaro umarnin su kai jami'ai garin sannan a kamo wadanda suka aikata wannan laifi dan hukuntasu, shugaba Buharin ya kara da cewa akwai jami'an soji na sama dana kasa suna aiki tukuru dan ganin sun kwato sauran yaran da suka rage a hannun wadannan mahara.

Ya kuma kara da cewa 'yan Najeriya  gaba daya na taya iyayen wadannan yara bakincikin abinda ya faru da yayansu.

No comments:

Post a Comment