Sunday, 11 February 2018

Shugaba Buhari yayi rashin 'yan uwa

A cikin wani sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar ta sanar da rasuwar da aka samu a dangin shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda kanwar dan uwanshi, Mamman Daura, Halima Dauda da kuma matar yayanshi A'isha Alhaji Mamman suka rasu kuma anyi jana'izarsu jiya Asabar a garin Daura mahaifar shugaban kasar.


Fadar shugaban kasa ta aike da wakilai daomin zuwa yin gaisuwa wanda shugaban ma'aikata Abba Kyari ya jagoranta, hadi da ministan jiragen sama Hadi Sirika da sauran wasu jami'an gwamnati.

Muna fatan Allah ya jikansu da dukkan sauran musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.


No comments:

Post a Comment