Friday, 16 February 2018

'Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara a 2019'>>inji sakataren gwamnati

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu saboda har yanzu babu madadinshi.


Boss Mustafa wanda me baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin siyasa ya wakilta lokacin da wasu matasa dake goyon bayan shugaba Buharin ya zarce sukayi gangami a Abuja, ya bayyana cewa zai isar da sakon nasu zuwa gurin shugaban kasar kuma sunyi tunani me kyau kamar yanda The Sun ta ruwaito.

Ya kara da cewa har yanzu babu wani rikakken dan takara daya fito wanda zai maye shugaba Buhari, duk wadanda ke ta yunkurin fitowa ko an basu dama babu wani abu da zasu iyayi saboda haka shugaba Buhari shine ya cancanci cigaba da jagorancin kasarnan.

No comments:

Post a Comment