Thursday, 15 February 2018

Shugaba Jacob Zuma na kasar Afrika ta kudu ya sanar da yin murabus

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ce ya sauka daga mulkin kasar bayan ya fuskanci matsin lamba daga jam'iyyarsa ta ANC.


Mista Zuma, wanda ya hau mulkin kasar tun a shekarar 2009, ya yi ta fuskantar zarge-zargen cin hanci.

Amma tun a watan Disamba ake matsa masa lamba cewa ya yi murabus, a lokacin da Cyril Ramaphosa ya maye gurbinsa a matsayin shugaban jam'iyyar ANC.
bbchausa

No comments:

Post a Comment