Tuesday, 6 February 2018

Tijjani Asase ya fara samun tallafi bayan da gobara ta kone gidanshi

Bayan da ibtila'in Gobara ya samu jarumin fina-finan Hausa, Tijjani Asase wanda yayi sanadiyyar konewar gidanshi kurmus. Jarumin ya fara samun tallafin kudi da kayan abinci  daga mutane daban-daban.'Yan uwa da abokan arziki ciki hadda tsffin jaruman fina-finan Hausa mata na cikin wadanda suka baiwa jarumin tallafi.
Ya rubuta a dandalinshi cewa:
"Salam barkanmu da safiya da mika godiyata ga iyayan gidana da yayyena wa'yan da suka tayani da alhini. wasu a waya wasu hargida wasa harda gudun mawa sutura da abinci wasu harda kudi nagode Allah yabar zumunci amin nagode"

Muna tayashi murna.

No comments:

Post a Comment