Saturday, 17 February 2018

Tusa ba kakkautawa da wani fasinja ya rikayi yasa jirgin sama yin saukar gaggawa

Wani jirgi daya tashi daga Dubai zuwa Armsterdam yayi saukar gaggawa wadda babu shiri saboda fada daya barke tsakanin fasinjoji dalilin tusa da wani dattijo ya rika yi ba kakkautawa kuma mutanen dake zaune kujera daya dashi sun ta rokonshi da ya dena amma yaki, hakan yasa aka fara zage-zage har fada ya barke.Rahotanni sun bayyana cewa fasinjojin sunyi kokarin yiwa masu gudanarwa na jirgin magana dan su hana mutumin yin tusar amma abu ya gagara, hakan yasa dole direban jirgin yayi saukar gaggawa a Vienna, Austria.
Bayan tsayawar jirgin sai 'yan sanda suka shiga suka fito da masu fadan su hudu, maza biyu mata biyu, sannan jirgin yaci gaba da tafiya.

Mata biyu da aka fitar daga cikin jirgin sunce ba'a musu adalci ba domin domin su basuyi fada ba kawai sun cewa ma'aikatan jirgin suyi wani abune akan tusar da mutumin yake yi.

Amma hukumar jirgin tace saidai su hau wani jirgin su karasa ta tafiyar tasu domin sun kawo har gitsi.

No comments:

Post a Comment