Tuesday, 27 February 2018

Usain Bolt ya saka hannu akan kwantirakin bugawa wata kungiyar kwallon kafa wasa: Zai yi wasa a Old Trafford

Shahararren dan wasan tsere da aka yi amannar cewa yafi kowa gudu a Duniya Usain Bolt ya bayyana cewa ya sakawa wata yarjejeniya hannu dan bugawa wata kungiyar kwallon kafa wasa, a ranar Lahadin data gabatane, Bolt ya  bayyana hakan kuma yace zai fadi ko wace kungiyace zai bugawa wasan a yau Talata.


Bolt ya bayyana cewa zai buga wasan neman kudin tallafawa kananan yara da majalisar dinkin Duniya zata shirya a filin wasa na Manchester United dake Ingila, Bolt dai zai buga wannan wasane tare da wasu shahararrun mutane da tsaffin 'yan kwallo da suka yi suna a Duniya.

Za'a buga wasan ranar goma ga watan Yuni idan Allah ya kaimu kuma yayi kira ga mutane da su fito su kalli wannan wasa musamman dan ganin an samu isassun kudin tallafawa kananan yaran.

Bolt yayi alkawarin cewa kungiyarshi ce zata yi nasara, kuma akwai wani salon murna na musamman da zai nuna idan ya samu nasarar zura kwallo a waccan ranar.

Bolt dai ya sha bayyana soyayarshi ta son buga kwallon kafa kuma ya bayyana Manchester United a matsayin kungiyar da yake so.

No comments:

Post a Comment