Monday, 19 February 2018

Wani ya cewa Ummi Zeezee ta daina yin Instagram tunda yanzu Kannywood bata yi da ita: Karanta amsar da ta bashi me zafi

Wani yayi kira ga tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee da cewa tunda yanzu masana'antar fim din Hausar batayi da ita da ta hakura da yin Instagram, Ummin ta mayar mishi da amsa me zafi.Daga cikin amsar data bashi tace, "Naga wannan tsohon mai mulki irin na fir'auna wanda ya jefa Najeriya a yunwa da talauci wannan wanda kuke goyan baya naga ai ya yi jika dani kuma bai daina Instagram ba balle ni"

2 comments:

  1. Ummi zeezee,amman kin bani mamaki ganin irin wannan kalaman da kika maida martani da su ga wanda yace"Ki bar yin istagram saboda kannywood bata yi dake".Shi mai maganar kadai ya kamata ki ambata banda shugaba Buhari.A a matsayinki na mai hankali,kuma mai ilimi.Wannan kalami naki da biyu,dama kina da niyyar fadin hakan.Allah Kyauta kuma Ya Fahimtar da ke.

    ReplyDelete
  2. Ire-iren wadannan kalamai basu kamace ki ba.Hada mulkin #fira'auna da na #Muhammadu_Buhari.Idan da mulkin soja ne,baki isa ki rinka irin wadannan kalaman ba ga Shugaba #Muhammadu_Buhari ba.

    ReplyDelete