Tuesday, 27 February 2018

Wani ya kunyata a masana'antar Kannywood: bayan da yayi gulma kuma aka jishi: Anawa Maryam, Umar da Garzali hassada

Da alama wasu ko kuma ace wani a cikin masana'antar fina-finan Hausa, yayi gulma kuma gulmar tashi ta fasu, da dama daga cikin jarumai a dandalinsu na sada zumunta da muhawara sunyi ta habaici suna cewa andai ji kunya wasu kuma suna tsinuwa da Allah wadai.


Saidai babu daya daga cikin jaruman da ya kama sunan kowa, a kwanakin bayane dai rikici yaso barkewa tsakanin yaran Ali Nuhu da na Adam A. Zango wanda kamin abin yayi nisa aka sasantasu.

Wani daga cikin masu bayar da umarni na masana'antar, Sanusi Oscar ya bayyana cewa sabbin jarumai guda uku watau, Maryam Yahaya da Umar M. Sharif  da Garzali Miko ne akewa hassada.

Ga abinda ya rubuta kamar haka:

"Wa Dannan Matasan Ba Wanda Bai San Suba A Wannan Lokacin' Duda Ance Iya Karkasara Aka Sansu' Sune Jaruman Da Suka Bada Ruwa Film Hause' Kuma Sune Sukai Tattaki Daga Nageria Har Zuwa Kasar Niger' Amma Ake Musu Hassada Ake Zaginsu Babu Laifin Tsaye Babu Na Zaune."

Muna fatan Allah ya kade fitina a ko inane.

No comments:

Post a Comment