Sunday, 11 February 2018

Wata kungiya me kin jinin addinin Islama ta hana a gina masallaci a gurin wasan Olampic a kasar Koriya ta Kudu

Organisers of the event confirmed there will be no prayer room PHOTO: REUTERS
Hukumar kula da yawan shakatawa ta kasar Koriya da Kudu inda ake wasannin Olampic na bana, tayi yunkurin ginawa musulmi da zasu j gurin wasan, Masallaci amma kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin kin jinin addinin Islama na kasar suka hana.


Hukumartayi la'akarin cewa akwai musulmai da zasu shiga kasar saboda da haka ta shirya zata gina musu masallaci kusa da gurin da za'a gudanar da wasan amma wadancan makiya Allan sukayi kememe sukace basu yarda ba. Har zama da su hukumar tayi kuma ta sakko kasa tace gurin ibadar da za'a gina bawai dan musulmi kadai za'a ginaba, haddama wadanda ba musulmai ba suma za'a gina musu bangarensu, idan zasu yi Ibadarsu suje suyi amma sai waccan kungiya tace bata yardaba, har ta bayar da misalin cewa idan gurin ba dan musulmi za'a ginashiba to ne zaisa a ware musu gurin yin Alwala?

Kungiyar dai tace idan aka sake akace sai an gina wancan masallaci to zatayi wata mummunar zanga-zanga a gurin wasan na Olampic, dole aka fasa ginin.

Aljazeera ta ruwaito wani musulmi wanda baya so a ambaci sunanshi yana cewa wannan abu beyi dadai ba amma ita wannan kungiya ta sani, hana gina wannan masallaci da tayi bazai hana musulmai yin Ibadaba, kawai dama za'a sama musu saukine.

A kasar ta Koriya ta kudu dai akwai abincin Halal da sauran wasu tanade-tanade da suka shafi musulmai da ake dasu dan jan ra'ayin musulmai masu yawon bude ido zuwa kasar.
Photo:reuters.

No comments:

Post a Comment