Wednesday, 21 February 2018

Wata miyar sai a makwabta: Kasar Singapore zata rabawa 'yan kasar rarar kasafin kudi da ta samu

Kasar Singapore tayi abinda ya dauki hankalin Duniya, bayan da Ministan kudi na kasar ya bayyana cewa kasar ta samu rara a kasafin kudin ta na shekarar 2017 kuma za'a rabawa 'yan kasar ne ranar kudin da aka samu kyauta.

Yawan kudin rarar da kasar Singapore din ta samu sun kai dalar Amurka biliyan bakwai da miliyan dari shida, kuma yanda za'a kasaftawa 'yan kasar kudin shine, duk wanda ya kai shekara Ashirin da daya zai samu dalar Amurka dari uku, kimanin kwatankwacin naira dubu dari da takwas kenan, ya danganta da yawan samunshi.

Wannan abu dai ba karamin birge sauran kasashen Duniya yayi ba, hakan ya nuna irin yanda shuwagabannin kasar suka iya gudanar da gwamnati da kuma amfani da kudaden da kasar ke samu yanda ya kamata.

Kasar Singapore dai ta kasance matalauciyar kasa wadda ke cikin halin ni 'yasu a shekaru Arba'in da suka gabata, amma cikin ikon Allah sai gashi sun samu shuwagabanni adilai, masu kishin kasa, sun dora kasar a turbar cigaba, itama ana damawa da ita ta fannonin cigaban zamani. 

No comments:

Post a Comment