Friday, 23 February 2018

'Ya Allah idan ta zarce na a matsayin gwamna Alherine ga mutanen jihar Kaduna kasanin zarce'>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi addu'ar cewa idan tazarce, cigaba da mulkin jihar Kaduna shine Alheri a gareahi da mutanen jihar, yana fatan Allah yasa ya zarce, gwamnan ya kara da cewa koda a lokacin da ya fito takarar gwamna a farko saida yayi irin wannan addu'a ya roki allah idan zamanshi gwamna Alherine Allah ya bashi.


Ga addu'ar da gwamnan yayi kamar haka:

"Kamar yadda na yi ta addu'a a 2014 in mulkin Jihar Kaduna da nake nema alheri ne ga mutanen Kaduna, Allah ya ba ni. Haka ma yanzu ina addu'ar in zarcewa na shi ne mafi alheri ga al'ummar Jihar Kaduna, Allah ya tabbatar mana. Burinmu shi ne mu yi abin da ya dace wanda zai amfani al'umma ba wai abin da aka saba yi ba.~ Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai."

No comments:

Post a Comment