Wednesday, 7 February 2018

Ya kashe makwauciyarshi saboda damunshi da tambayar yaushe zai yi aure

Wani mutum me suna Faiz Nurdin me shekaru ashirin da takwas a Duniya ya kashe makwauciyarshi me dauke da juna biyu 'yar shekaru talatin da biyu me suna Aisyah a kasar Indonesia saboda damunshi da tambayar cewa yaushe zaiyi aure da take yi akai-akai.Kamar yanda rahotanni suka bayyana matar ta hadu da Nadir ta kuma sake mai tambayar"yaushe zaka yi aurene, duk sa'anninka sunyi sun barka?", ashe tambayar tawa Nurdin zafi, ya riketa Zuciya, da yammacin ranar da suka yi maganar sai Nadir ya kaiwa Aisyah ziyara gidanta, inda ya shammace ta ya shaketa ta mutu. Bayan kashe ta sai ya sace wasu 'yan kudinta da wayar salula ya tsere.

Amma jami'ai sunyi nasarar kamashi, bayan da aka harbeshi a kafa lokacin da yake shirin tserewa.

Ana sa rai dai mutumin zai gamu da hukuncin daurin rai da rai.
detik.com

No comments:

Post a Comment