Wednesday, 7 February 2018

YA SHIGA MUSULUNCI SABODA SHUGABA BUHARI


Wani mai suna Rabaran Simon Paul Fada ne a cocin Ingilika dake Shagamu a jihar Ogun, ya baiyana  dalilin da yasa shi shiga musulunci kamar haka:


"Lokacin da Shugaba Muhammad Buhari ya je wajen jinya a kasar waje (Ingila) kungiyar kiristoci ta tara mu limaman coci-coci aka umurce mu da yin azumi da wasu addu'o'i da zummar kada shugaba Muhammad Buhari ya dawo da rai, ni kuma na ce zanyi, amma idan har ya dawo da rai zan koma musulun ci, ina zaune ina kallon Talabijin kawai ran nan sai na ga labari akan dawowar shugaba Muhammad Buhari lafiya kalau, kawai sai na karbi musulunci inda aka bani suna Abubakar".

 Yanzu haka ya samu mafaka a garin Asaba sakamakon halin firgita da ya shiga na barazana da rayuwar sa da 'yan uwansa ke yi.
Rariya

No comments:

Post a Comment