Saturday, 17 February 2018

Yadda Boko Haram da talauci suka 'wawure' kudin JAMB

Hukumar da ke shirya jarrabawar shiga jami'a a Najeriya (JAMB), ta ce ta kama wasu jami'anta da dama da hannu a almundaha da kudaden hukumar a jihohi daban-daban, tun daga 2015 zuwa watan Agustar 2016.


Mai magana da yawun hukumar Fabian Benjamin, ya shaida wa BBC cewa hukumar ta gano hakan ne sakamakon wani kwamiti da ta kafa tun bayan zamowar Farfesa Ishaq Oleyede shugabanta, bayan ya gano cewa ana tafka badakala wajen sayar da katin yin rijistar jarrabawar wato Scratch Card.

Tana binciken miliyoyoin kudin da aka samu ne daga katin duba sakamakon jarabawar da dalibai suka dauka daga shekarar 2015 zuwa 2016.

Mista Benjamin ya ce wannan dalili ne ya sa aka kafa kwamitin bincike don gano irin badakalar da aka yi ta yi a hukumar don dakatar da faruwar hakan da kuma daukar matakan da suka dace.

A jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, an samu babban jami'in hukumar, Sanusi Atose, da hannu a salwantar da naira 613,000, wanda ya ce yaki da kungiyar Boko Haram a yankin ne ya jawo.

A lokacin da Mista Atose yake ba da ba'asi ya ce "tashin hankalin Boko Haram ne ya sa bai san inda kudin suke ba."

Jami'in ya ce takardun banki da rasitan duk sun lalace sanadiyyar hare-haren kungiyar, inda ya ce hakan ya sa ba shi da wata shaidar lissafe-lissafen kudaden da aka samu.

Sai dai shugaban hukumar Farfesa Oleyede ya yi watsi da hanzarinsa, inda ya ce wani yunkuri ne kawai na zamba.

"Ka je ka biya gwamnati kudinta nan da mako daya, idan kuma ba haka ba kana cikin matsala," in ji shugaban kwamitin binciken.

Hakazalika, babban jami'in hukumar a jihar Kogi Daniel Agbor, ya ce ya "kashe naira miliyan bakwai wajen taimakawa wadansu ma'aikata wadanda talauci ya yi wa kanta."

Har ila yau jami'in ya ce wadansu daga cikin katuna duba jarabawar da aka aika jihar wadansu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace su. Halin da ake ciki a ofisoshinmu shi ne akwai talauci kuma akwai kudi a tare da mu," in ji babban jami'in hukumar yayin da yake ba da ba'asi a gaban kwamitin.

Mista Agbor ya ce "mutum yana bukatar taimakon Ubangiji don Ya tsare shi daga yin sata saboda kudi na sauya mutum. Mun yi aron kudin ne kuma ba ni kadai ba ne, zan ba da sunayen duk wani da yake da hannu a wannan zambar."

Babban jami'in hukumar a jihar Nasarawa Labaran Tanko shi ma cewa ya yi naira miliyan 23 na hukumar sun salwanta a hannunsa ne "bayan motarsa ta kama da wuta."

Haka dai manyan jami'an hukumar na jihohin Kano da Gombe da Edo da Ondo da sauransu suka kasa yin bayanin yadda suka yi da miliyoyin kudin hukumar daya bayan daya.

Wannan batun ya fara mamaye kafafen yada labarai a fadin Najeriya ne bayan wata jami'ar hukumar a jihar Benue, Philomena Chieshe, ta yi ikirarin cewa wani maciji ya hadiye naira miliyan 36 na hukumar.


Kuma tun bayan haka ne ake ci gaba da samun bayanai masu daure kai daga jami'an hukumar wadanda ake zargi da aikata zamba.

Hukumar ta dakatar da dukkan jami'an hukumar da ake zargi da almundahanar kuma ta mika wa 'yan sanda batun don fara bincike kan al'amarin, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Fabian Benjamin ya tabbatar wa BBC.Hakazalika ya ce hukumar ta rubuta rahoto kan wadanda ake zargin kuma ta mika shi ga ma'aitakar ilimi. "Da zarar ta amince to za mu dauki matakan da suka dace kan wadanda ake zargin kamar yadda dokokin aikin gwamnati suka tanada," in ji shi.

Cin hanci da rashawa da kuma almundahana da kudin gwamnati dai ya zama tamkar ruwan dare a Najeriya, sai dai tun bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari mulki ya fara yaki da wannan dabi'a kamar yadda ya yi alkawari lokacin neman zabe.

A yanzu dai ba za a iya cewa an daina cin hanci baki daya ba a Najeriya, amma akwai alamun cewa ana samun nasara a yaki da dabi'ar wacce Shugaba Buharin ke yi, ta hanyar bankado duk wanda aka samu da laifin.
bbchausa.
No comments:

Post a Comment