Wednesday, 28 February 2018

'Yan Afrika mazauna kasar Isra'ila sunyi zanga-zanga saboda ance su bar kasar: sunce sun kwammace da zaman gidan yari dasu dawo Afrika

'Yan kasashen Afrika dake neman mafaka, mafi yawanci wanda suka fito daga kasashen Sudan da Eritrea, sun yi zanga-zanga a kasar Isra'ila akan korar da kasar tace zata musu, kasar dai ta Isra'ila ta ce ta basu nan da zuwa daya ga watan Afrilu su bar kasar kuma duk wanda ya yarda zai tafi, to zama a hada mishi da kudi dalar Amurka dubu uku da dari biyar, kimanin sama da naira miliyan daya da dubu dari biyu kenan.To amma bakaken fatar basu yarda ba, sun bayyana wannan kora da za'a musu a matsayin nuna wariyar launin fatane kawai, wannan yasa suka yiwa fuskokinsu farin fenti inda suke cewa to gashi muma mun zama farar fata saboda haka kada a koremu.
A wasu rahotanni da suka fito kwanakin baya, bakar fatar da suke can kasar ta Isra'ila sun bayyana cewa sun kwammace da zaman gidan yari acan Isra'ilar da su dawo gida Afrika.

No comments:

Post a Comment