Friday, 2 February 2018

Yanda uba ya rika lalata da diyarshi kamin ya bata kudin abinci

Labarin wannan yarinyar nada ban tausai da matukar takaici, Sunanta Rukayya, kamar yanda ta bayyana, shekarunta sha biyar da haihuwa kuma tana makarantar sakandire, aji hudu, ta bayyana cewa tun tana 'yar shekara goma sha daya mahaifinta ke lalata da ita wai akan abinci.


Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, wannan labari da matukar takaici yake, yarinyar saboda yarinta ta rika baahi hadin kai har Allah yasa mahaifiyarta ta gano, bakin cikin hakan ya kashe mahaifiyarta, ta koma gurin kakarta, wai abincin da zai rika basu ita da 'yan uwanta, duk lokacin da taje kar bowa sai yayi lalata da ita tukuna ya bata.

Mansurah Isah ta hadu da wannan  yarinya, kamar yanda ake iya gani a wadannan hotunan, kuma dalilin haka kuma har ta fara samun tallafi daga gidauniya mawaki, Ali Jita, muna fatan Allah ya saka musu da Alheri su duka.

Ga yanda yarinyar ta bayar da labari da abin ya isheta:

Gaskiya Mansura wannan ba karamin Jihadi kika yi ba, Allahne kawai zai biyaki. Amma wannan abu yayi muni. Zunu bi zunubi ne amma idan kaji wani abin Toh, sai Allah.

No comments:

Post a Comment