Monday, 26 February 2018

'Yar Shekara 15 Ta Bayyana Yadda Ta Tsallake Rijiya Da Baya A Harin Makarantar Mata Dake Dapchi A Jihar Yobe

Wata yarinya 'yar shekara 15 dalibar makarantar mata dake Dapchi a jihar Yobe ta bayyana yadda ta tsallake rijiya da baya a harin da 'Yan Boko Haram suka kai makarantar tasu ranar Litinin din da ta gabata inda suka kwashe daliban mata sama da 100 suke garkuwa da su.


Da take zantawa da jaridar The Nation, Yarinyar mai suna Amina Malam Usman tace: "Lokacin da 'yan Boko Haram din suka zo makarantarmu mun zaci sojoji ne, saboda sun yi shiga irin ta sojoji. Sai muka sheka a guje,sai daya daga cikinsu ya kira mu. Sai wani daga cikinsu ya ce inzo kusa da motar. 

"Lokacin da na zo kusa da motar, sai daya daga cikinsu ya fara yi mini dariya, na kara matsawa kusa da su, ina zaton sojoji ne. 

"Daga nan sai jikina ya ba ni cewar wadannan ba sojoji bane, sai na yi kokarin shekawa a guje inda wani daga cikinsu ya yi kokarin kama ni sai na subule masa amma ya samu ya janye hijabi na.

"Sai na yi sauri na subule hijabin na bar masa na runtuma a guje. Na yi tsammanin na mutu.

"Sai suka shiga dakunan kwananmu na dalibai, amma tuni wasu sun runtuma da guda cikin jeji.  Na yi gudun fitar rai na akalla kilomita 5 inda na tarar da wani kauyen Fulani da ake kira Miligiya na buya a nan"

Lokacin da aka tambayi Amina ko za ta iya tuna ko dalibai nawa ta gani a cikin motar wadanda suka zo yin garkuwa da su sai ta ce: "Gaskiya suna da yawa domin akalla wadanda na gani a cikin motar a lokacin za su kai kimanin 50"

Ta ce a lokacin ji tayi ina ma a ce mala'ikan mutuwa ya zare ranta a lokacin da ta fahimci cewar wadannan mutanen 'yan Boko Haram ne. 

Ta ce ita a yanzu gaskiya ba tajin za ta iya sake komawa wannnan makarantar ta su dake Dapchi.
Real Sani Twoeffect Yawuri

No comments:

Post a Comment