Thursday, 8 February 2018

Yayin da ake tunanin komai ya wuce: General BMB ya mayarwa da Yakubu M. Kumo martani

Ana tunanin rikicin cacar baki a masana'antar fina-finan Hausa ya kare, bayan da akawa Ali Nuhu da Adam A. Zango sulhu a daren jiya, haka shima Bello Muhammad Bello, General BMB ya fito ya bayyana cewa yayi shiru, to amma ya sake yin magana, ya mayarwa da Yakubu M Kumo martani akan rubutun da yayi na cewa, Bellon be kyautaba da yake tambayar Alin cewa ya akayi mahaifiyarshi ta auri wanda ba musulmiba.


 Bellon yace dalilin da yasa bazai mayarwa da Yakubu da martani ba shine saboda ya taba mishi halaccin da bazai mantaba, inda har ya kawo shahararren Hadisin bayin Allahnnan da suka shiga kogon dutse fake ruwa ya rufe dasu, kowane ya fadi abin Alherin da ya taba yi dan neman yardar Allah sannan suka samu kubuta, Bellon yace to tunda Allah ma daya haliccemu yana sassautawa mutum idan yayi Abin Alheri shima shiyasa bazai mayarwa da Yakubu M. Kumo martani  ba a rubutun da yayi na son kai da goyon bayan Ali Nuhu, kamar yanda Bellon ya bayyanashi.

To saidai duk da haka Bellon ya cewa Yakubun da alama be iya aikinshi na rubutuba, inda har ya bashi shawara yaje gurin wasu sanannun masu rubutu na fina-finan Hausa su koya mishi yanda akeyi. Ya kuma kara da cewa a iya saninshi Yakubun baya rubutawa kamfanin Ali Nuhu na FKD labarin fim to amma ga dukkan Alamu tunda yanzu yayi tarayya da Ali Nuhun wajan zama makiyanshi(Bellon) to yasan cewa zai iya fara rubuta musu fim, tunda makiyin makiyinka abokinkane.

A karshe Bellon yace yana ganin girman Kumon kuma zai cigaba da girmamashi.

Wannan dai ya fito da wata daddaddiyar rashin jituwa wadda ga dukkan alamu ke tsakanin Bellon da Alin sai muce Allah shi kyauta ya kuma sa su fahimci juna.

No comments:

Post a Comment