Saturday, 17 February 2018

'Zan iya kashe kaina idan....'>>Obasanjo

A wata ziyara da ya kai jihar bayelsa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi bayanin cewa zai iya sargafe kanshi da igiya ya mutu matukar akace Najeriya ta rasa Alkibla, ya kara da cewa wannan nema yasa duk lokacin da ya ga anyi abu ba daidai ba baya iya yin shiru sai yayi magana.


Obasanjo ya kara da cewa ko da mutum ne ace bashi da buri babu alkibla to ba shakka rayuwarshi zata tabarbare, ya ce tabbas akwai abubuwan da ya kamata ace shuwagabannin Najeriya suyi amma basa yi, to amma hakan bazai sa kowa ya rungumi hannu da nuna rashin kula ba.

Yace yayi iya kokarinshi wajan yin amfani da damar daya samu yanda ya kamata lokacin yana shugaban kasa, duk da cewa bai yi komai dari bisa dari ba amma beyi nadamar abubuwan da yayi ba a wancan lokacin.
Sun

No comments:

Post a Comment