Wednesday, 28 February 2018

Zan Yi Azumin Kwanaki Uku Domin Yi Wa Gwamnatin Buhari Addu'ar Samun Nasara, Cewar Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai gaza wajen tafiyar da mulkin Nijeriya ba, matsalar Nijeriya a Arewa take. "Idan manyan shugabannin Arewa za su ji tsoron Allah su gyara halayensu to gaba daya Nijeriya za ta iya gyaruwa, amma idan ba su gyara ba to nan da shekaru 50 masu zuwa Nijeriya ba za ta gyaru ba.Amma ina sa ran idan Buhari ya kwashe shekaru 8 yana mulkin kasar nan shakka babu zai gyara kashi 90% cikin 100% na matsalolin Nijeriya kuma a matakan da yake dauka idan ba shi ba ban ga wanda zai iya amfani da su ba, saboda haka masu cewa Buhari ya gaza karya suke yi kuma matsorata ne idan kuma basu da tsoro su zo su fadi a gabana su gani kuma nima na kuduri aniyar yin azumin kwana 3 don yiwa Buhari addu'a".

rariya

No comments:

Post a Comment