Wednesday, 14 March 2018

Abdulmumini Jibril ya koma Ofis: Na koyi darasi da yawa>>injishi

Dan majalisar wakilai, daga jihar Kano, Abdulmumini Jibril kenan a ofishinshi bayan ya koma aiki a majalisa dalilin dage dakatarwar da aka mishi, Abdulmumini ya bayyana jin dadinshi akan komawarshi aiki kuma yace ya koyi darussa da yawa akan wannan abu da ya faru dashi.Ga abinda ya bayyana kamar haka:

"Yau na koma Majalisa a matsayin Dan Majalisa Mai Wakiltar Mazabata tare da cikakkiyar dama da 'yancin yin aiyukan da Majalisa da dokar zaman Majalisa ta bani. Hakika illimin da na samu cikin shekaru biyun nan ya shiryar dani sabon jajircewa da kara damara don bautawa al'ummata da kasa baki daya. Wannan wata hanya ce da ba zan taba kauce mata ba da yardar Allah. Ina matukar godiya da goyon bayanku, godiyar  da baki ba zai iya  fasaltata ba.

 Hon Abdulmumin Jibrin kofa"
No comments:

Post a Comment