Monday, 5 March 2018

'Abinda kullun na tuna yake min kududu a zuciyata'>>Obasanjo

A yaune tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi inda ya cika shekaru tamanin da daya da haihuwa, a wani jawabi da yayi lokacin da aka shiryamai liyafa dan murnar wannan rana, obasanjo ya bayyana abinda kullum idan ya tunashi yake jin bakin ciki a zuciyarshi.


Obasanjo yace mutuwar iyayenshi tana sashi cikin bakin ciki sosai a duk lokacin da ya tunata musamman ganin cewa basu rayu suka ga irin daukakar da Allah ya mishi ba, yace abin yana matukar damunshi, yaso ace sun kawo lokacin da ya samu Duniya domin suma ya jiya musu dadi.

Yace amma yasan cewa, kamar yanda wata karin magana ta Yarbawa ke fadi cewa, duk matattu su kanzo su duba masoyansu dan ganin irin rayuwar da suke ciki bayan mutuwarsu, da wannan yace yasan iyayenshi suna can cikin kabarinsu suna farin ciki da irin daukakar da Allah ya mishi.

Obasanjo ya kuma godewa duk na kusa dashi da masu taimakamishi akan harkokinshi na yau da kullun yace duk suna mai biyayya yanda ya kamata kuma sun bayar da gagarumar gudummawa ta kasancewarshi a inda yake a yanzu.

Haka kuma yace, halin da Najeriya take ciki, Allah be sakawa 'yan Najeriya wani mummunan abuba, idan muka ga wani mummunan abu ya faru damu to sai mu tambayi kanmu menene mukayi ba daidaiba, kamar yanda jaridar Premium times ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment