Thursday, 15 March 2018

Abubuwa 11 da suka faru a bikin Fatima Ganduje da Idris Ajimobi da suka dauki hankulan mutane

Daurin auren 'ya'yan gwamnonin jihohin Kano da Oyo, Fatima Abdullahi Umar Ganduje da mijinta, Idiris Abiola Ajimobi ya dauki hankulan mutane sosai a kasarnan, musamman a Arewa, Abu na farko a wannan biki da ya fara daukar hankulan mutane shine.

Auren 'ya'yan gwamnoni kuma ba kabila daya ba: Tun da labarin cewa gwamnan jihar Kano zai aurar da diyarshi ga dan gwamnan jihar Oyo ya bayyana wasu suka fara buda baki cikin mamaki da cewa gwamnan zai aurawa diyarshi bayerabe. Wasu kuwa yabawa da wannan abu sukayi inda sukace ai hakan zai kara hadin kai da zumunci tsakanin Arewa da kudu, musamman kabilar yarbawa.

Daga nan kuma sai kayan lefen da aka kawowa Fatima: Suma sun dauki hankulan jama'a musamman mata inda aka rika bude baki yayin da akaga akwatuna kala-kala kuma shima an yaba sosai dan shi yabonshi yafi kushenshi yawa.

Kusa da biki kuma sai wasu hotuna da Idris din yake sakawa matartashi zobe a hannu suka bayyana, suma wadannan hotunan sun ja hankulan mutane akai ta tsokaci akai.


Daurin auren da akayi ya dauki hankulan mutane sosai dan kuwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Bola Tinubu, jigo a jam'iyya me mulki ta APC ne suka wa ango da amarya wakilci da waliccci sai kuma sarkin Kano,  Muhammad Sanusi da ya daura aure, gwamnoni kusan ashirine da sauran masu fada aji na kasarnan suka halarci daurin auren. A bin ya kayatar sosai to amma ta bangaren shugaban kasa, suka yasha dalilin halartar wannan dairin aure. Masu sukar sunce baikamata ace yaje daurin auren ba yayinda ga jihohi da ake fama da rikici da bai ziyartaba.

Sadakin Fatima na dubu Hamsin ya dauki hankulan mutane sosai wanda har saida shi kanshi uban Ango, Gwamna Ajimobi yayi barkwancin cewa tunda haka aure yake da sauki a Arewa to a karawa dan nashi wata matar.

Bayan daurin aurene sai wani hoto ya bayyana da ya nuna ango Idris ya dakumi Matarshi inda ya sumbaceta, wannan abu ya matukar dauki hankulan mutane sosai inda akai ta cece kuce akai wasu suka rika kiran ina hukumar Hizba ne ko kuwa 'ya'yan talakawa kadai akewa hukunci idan sunyi irin wannan?.

Rashin jin duriyar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da ma sauran malamai na Arewa akan wannan batu, musamman lura da cewa lokacin da Rahama Sadau ta rungumi mawaki Classiq an hukuntata ya jawo cece-kuce inda wasu suka rika zargin malaman da cewa duk suna gani amma sunki yin magana akai saboda 'yar gwamnace.

Maganar da aka ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso yayi akan auren inda ya danganta Fatima Ganduje da cewa auren bazawarane shiyasa beyi armashiba, ta jawo cece kuce, inda wasu suka goyi bayanshi wasu kuwa sun bayyana cewa be kamata yayi wannan magana ba.

Maganar da tauraron fina-finan Hausa, T. Y Shaban yayi akan wancan hoto inda ya zargi abokin aikinshi Nura Hussain da kin yin magana akan abinda diyar gwamnan tayi amma yana gaba-gaba lokacin da Rahama Sadau ta rungumi mawaki Classiq ta jawo cece kuce inda da yawa suka bashi rashin gaskiya na cewa ba hurumin Nurane yayi magana akan abinda diyar gwamna tayi ba.

Ana cikin wannan sai kuma ga wasu hotunan bidiyo suka bayyana, Fatima Ganduje nata tika rawa acan jihar Oyo inda shagalin biki yaci gaba ta bangaren Ango, yanayin rawa da kuma shigar da Fatimar tayi ya jawo mata dama iyalanta surutai kala-kala inda wasu suka rika cewa ba tarbiyya, wasu ma cewa sukayi da wuya idan cikin hayyacinta take, domin amarya ace ta feke ido a gaban mutane tana ta tika irin wannan rawa ta wuce misali, watakila ma kwaya tasha.

Ana haka sai kuma ga wani mawaki harya tsarawa Fatimar waka, wai anki auren zawarawa anyi auren zawara, wannan waka tasha kushe a wajen wasu inda suka bayyana hakan da cewa cin fuskane gurin amaryar, wasu kuwa yabawa sukayi da wakar.

Ya zuwa yanzu dai da alama shagali ya kare.

Muna fatan Allah ya basu zaman lafiya.

No comments:

Post a Comment