Saturday, 10 March 2018

Akon na son tsayawa takarar shugaban kasar Amurka

Tauraron mawakin kasar Amurka, da ake kira da Akon ya bayyana muradinshi na son tsayawa takarar shugaban kasar a shekarar 2020, da yake hira da manema labarai, Akon yace idan zai tsaya takarar zai bukaci me kamfanin Facebook Mark Zuckerberg ya tsayamai a matsayin mataimakinshi.


Akon dai yana ta kokarin taimakawa al'umma musamman a Afrika, har dama can kasar ta Amurka da suka shiga cikin wani hali na bukatar taimakon, wasu na ganin wannan wata hanyace da yake bi wajan tallata manufarshi ta siyasa.

No comments:

Post a Comment