Sunday, 25 March 2018

'Allah ka bani mijin da zai killaceni: Bani son miji mara kishi'>>inji wannan budurwar

A cikin wannan zamani da idan aka tashi aure ko murnar zagayowar ranar haihuwa kai wasu ma ko ciki suka samu haka zaka ga ana ta nunawa Duniya, hotunan kamin biki a wasu lokutan ma hadda mazajen ko kuma ace suna sane, wata baiwar Allah ta bayyana cewa ita bata son irin namiji mara kishi, me soyayyar zamani da zai ta nunawa Duniya ita a matsayin matarshi, wanda bazai ji koda kanshin Aljannaba


Ta roki Allah ya bata miji me kishi da zai killace ta kuma me kaunarta, da sauran 'yan mata gabata daya.

Wannan addu'a tata ta birge mutane musamman mazaje inda wasu suka rika fadin ashe akwai sauran irinsu a wannan zamani da idan miji yana kula da matarshi irin yanda addini ya tana da sai ace be son cigabanta?.

Muna fatan Allah ya amsa wannan addu'a tata.

No comments:

Post a Comment