Monday, 12 March 2018

Allah ya haskaka zuciyar wani ba'amurke ya amshi addinin musulunci

Allah ya haskaka zuciyar wani ba'amurke  ya amshi addinin musulunci, mutumin me suna Marcus Prince ya bayyana musuluntarshi a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda yace, jiya ce ranar da tafi kowace rana a rayuwata saboda na amshi kalmar shahada na zama musulmi.


 Yace yana godiya ga dukkan wadanda suka taimaka wajan ganin ya amshi kalmar shahadar. Ya saka hotunanshi tare da abokanshi da suke taya shi murna.

Muna mishi fatan Allah ya kara fahimtar dashi addinin ya kuma karo mana irinshi da yawa.
No comments:

Post a Comment