Sunday, 25 March 2018

'Allah ya isa ban yafe ba'>>Rahama Sadau ta gayawa wani shafi da ke wallafa labarun karya akanta

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta nuna bacin ranta akan labarin da shafin watsa labarai na Naija.com ya buga dake cewa wai ta yi karin bayani akan wanda zata aura, Rahama ta karyata labarin sannan kuma tace wannan karo na uku kenan suna mata irin wannan karyar.


A karshe dai Rahama ta musu Allah ya isa inda ta kara da cewa bata yafe musu ba.

To saidai da dama daga cikin masoyanta da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wanna  lamari sunyi kira a gareta da tayi hakuri ta daina kula irin wadancan abubuwa dama idan akace mutum ya samu daukaka dole a rika mishi irin wannan.


No comments:

Post a Comment