Wednesday, 21 March 2018

'Allah ya tsinewa 'yan luwadi: Idan anji haushi a kaini kotu ina da hujja>>General BMB

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello yayi habaici akan wasu da ya bayyana da cewa masu luwadi ne inda yace an daina yi a Jos saidai su dinga binsu can din anayi, ya kuma ce wai ana barna amma mutane na cewa suyi shiru, saboda haka shi bazaiyi shiru ba.


A karshe General BMB yace Allah ya tsinewa masu Luwadi kuma ya rufe kalamanshi da cewa shi so yake a kaishi kotu dan ya tara 'yan jaridu ya bayyana ko su wanene da hujjarshi akan wanda aka yi abin dashi.

Wannan batu ya dauki hankulan mutane da dama inda wasu suka rika kiran Bellon da cewa hakan be kamata ba dan tozarta mutum babu kyau.

Dangan taka dai tayi tsami tsakanin Ali Nuhu da Bellon tun bayan wata 'yar hatsaniya da aka samu taakanin yaran Alin da Bellon inda Bellon yayi zargin cewa Alinne yake turo yaranshi suna mai rashin kunya.

Amma har ya zuwa yanzu Alin be kula Bello ba.

A kwanakin baya mutanen gari sun rika yiwa jaruman fim din zargin cewa akwai 'yan luwadi a cikinsu wanda hakan yasa Adam A. Zango ya fito a wani gidan talabijin ya dora Qur'ani akai yasha rantsuwar cewa shi ba dan luwadi bane. Allah shi kyauta.

Ga abinda Bellon yace kamar haka:
"
Kaji ana my Son, my Father! Anjima kaji ana kwakule son din.
Wallahi sai dai su dinga binku can din amma kun daina yi a Jos.
Wai yanzu bayin ALLAH ana barna kuna cewa muyi shiru! ALLAH ya tsinewa 'yan Luwadi.
Duk na Annabi da mai adawa da luwadi yace Ameen."

No comments:

Post a Comment