Saturday, 17 March 2018

Allah ya yiwa Sanata Ali Wakili Rasuwa: Bukola Saraki, Yakubu Dogara sun kadu da jin rasuwarshi

A yaune Allah ya yiwa sanata me wakiltar Bauchi ta kudu, sanata Ali Wakili Rasuwa, ya rasune bayan yayi fama da gajeruwar rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru hamsin da takwas a Duniya, kamin rasuwar tashi shine shine shugaban kwamitin rage radadin talauci na majalisar sanatoci.Da yake magana akan rasuwar ta sanata Ali wakili, Kakakin majalisar dajjitai Bukola Saraki ya bayyana mamacin a matsayin abokin aiki na gari wanda ya bayar da gudummuwa sosai wajan cigaban al-umma, Saraki yace a lokacin da ya samu labarin rasuwar sanata Ali Wakili yana kan hanyarshice ta zuwa gidan mataimakin shugaban kasa dan tayashi murna akan baikon da akawa diyarshi amma sai ya juya ya nufi gidan mamacin inda yayi ma iyalanshi gaisuwa.
Kakakin majalisar wakilai ma, Yakubu Dogara ya bayyana cewa ya kadu sosai da jin rasuwar ta sanata Ali Wakili inda shima ya bayyanashi a matsayin wanda ya kawo cigaba ga al-ummar mazabarshi ta Bauchi da ma mutanen Najeriya baki daya.

Muna fatan Allah ya jikanshi yakai Rahama kabarinshi idan tamu tazo yasa mu cika da Imani.

No comments:

Post a Comment