Tuesday, 6 March 2018

Almubazzaranci Ne Gwamnoni 24 Sun Kwashi Kansu A Jirgi Su Je Daurin Aure Yayin Da Talakawa Ke Cikin Mawuyacin Hali, Cewar Sheik Ahmad Gumi

Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya soki almubazzarancin da Shugabanni suka yi wajen daurin aure a Kano.

Fitaccen Malamin, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na facebook, ya kara da cewa Allah zai tambayi Shugabanni game da talakawa. Ya ce bai kamata ba a lokacin da talakawa ke cikin mawuyacin a hali a asibiti,gidajen su da sauran wurare, amma gwamnoni sin kwaahi kansu a jirgi su tafi daurin aure. Ya kara da cewa kudin man jirgin da aka yi amfani da shi zuwa daurin auren, ya isa a toshe waau matsalolin talakawa da su.


Malamin yace duk da N50, 000 ne kurum sadakin auren, an yi muguwar barna.

Haka kuma, Sheil Gumi ya koka da yadda ma'auratan suka rika daukar hotunan assha.
rariya.

No comments:

Post a Comment