Thursday, 1 March 2018

Aminu S. Bono ya yiwa jaruman fim din Hausa budaddiyar wasika: Na yi mamakin irin yanda jarumai 'yan kadanne suka je daurin auren diyar Ibro

Me bayar da umarni a fina-finan Hausa, Aminu S. Bono ya fitar da wata budaddiyar wasika inda yayi kira ga jarumam fim din Hausa da suke fada ko gaba da juna da su kai zuciya ne sa domin Duniyarnan ba komai bace, yayi misali da marigayi Ibro inda yake cewa duk daukakarka baka kai Ibro ba saidai kuzo da ya dashi amma yau gashi babu shi ya rasu.


Yace abin mamaki kwanakin baya aka aurar da diyar ta Ibro amma kadanne daga cikin abokan aikinshi suka halarci gurin daurin auren, wanda yace da yana da rai da ba haka ba.

Ya kara da yin nasihar cewa jaruman su rika hakuri domin dama dole a samu wanda zai zage ka ko kuma yayi gulmarka amma idan ka mayar da Alheri da sharri sai ka samu koyi da manzon Allah wanda dama dashi kowa yake hankoron koyi.

A kwanannan ne dai aka samu wata magana ta fito da wani wanda ba'a bayyana ko wanene ba yayi akan wasu jarumai, haka kuma a kwanakin baya an samu rashin jituwa tsakanin yaran Ali Nuhu da na Adam A. Zango.

No comments:

Post a Comment