Friday, 16 March 2018

An bude kamfanin sarrafa shinkafa 'yar gida na farko a jihar Kaduna

An bude kamfanin yin shinkafa 'yar gida da aka noma a Najeriya na farko a jihar Kaduna, gwamna Malam Nasiru El-Rufai na jihar ya taya masu kamfanin murna inda yace wannan irin yanda jam'iyyar APC ke kokarin ganin samar da abincin da ake amfani dashi kenan a gida Najeriya, ba sai an shigo dashi daga kasar waje ba kenan.Gwamnan yace jihar ta Kaduna zata cigaba da bayar da dama ga 'yan kasuwa dan su zuba jari a jihar.


No comments:

Post a Comment