Saturday, 24 March 2018

An ci gaba da shagalin bikin Fatima Dangote da Jamil M.D Abubakar a Legas: Bill Gates ya halarta

Kamar yanda bayanai tun farko suka shaida mana cewa a shagalin bikin Fatima Aliko Dangote da Angonta, Jamil M.D Abubakar da za'a yi a birnin Legas, daya daga cikin manyan bakin da zasu halarci wannan guri hadda me kudin Duniya, Bill Gates, to abu ya tabbata, an ci gaba da shagalin bikin ma'auratan a otal din Eko dake Legas kuma manyan baki ciki hadda Bill Gates din sun halarta.Amarya da Ango sun sha kwalliya irin ta 'yan zamani, abokai 'yan uwa da abokan arziki, masu fada aji da sanannun mutane sun halarci gurin shagalin, muna fatan Allah ya sanya Alheri.

No comments:

Post a Comment