Saturday, 31 March 2018

An daura auren kanin A'isha Buhari: Zahara Buhari ta dauki hankulan mutane a gurin bikin

A jiyane aka daura auren kanin matar shugaban kasa, Hamza Halilu Ahmad da matarshi, Hadiza Jika a babban masallacin birnin tarayya Abuja, shugaban kasa da wasu gwamnoni da ministoci sun samu halartar daurin auren, bayan nan an yi liyafar cin abinci a fadar shugaban kasa inda har diyar shugaban kasar, Zahara Buhari ta halarta.


Da yawan mutane dai hankalinsu ya karkata zuwa ga Zahara Buhari inda aka rika magana akan cikin da take dauke dashi da ya bayyana, aka kuma ta yi mata fatan Alherin Allah ya raba lafiya.
Muna fatan Allah ya ba Ango da Amarya zaman lafiya, ita kuma Zahara Buhari Allah ya sauke ta lafiya da sauran mata masu ciki.

No comments:

Post a Comment